Friday, December 5
Shadow

Masana a Amurka sun ce hare-haren kasar Israyla kadai ba zai iya hana kasar Ìràn mallakar makamin kare dangi ba saida taimakon Amurka

Wani Rahoto daga kafar Newsweek yace masana a Amurka sun ce hare-haren kasar Israyla kadai ba zai iya hana kasar Iran mallakar makamin kare dangi ba.

Rahoton yace dole sai kasar Amurkar ta taimakawa Israyla.

Rahoton yace ko da ma Amurkar ta taimakawa Israylan, idan dai ba kawar da gwamnati me ci suka yi daga kan mulki ba, za’a dakatar da shirin ne na dan wani lokaci amma za’a ci gaba.

Dan haka rahotan yace ko da basu yi nasarar kawar da Gwamnatin kasar daga kan mulki ba, su gurguntata ta yanda mutanen kasar zasu tashi tsaye su nemi sauyin gwamnatin Dimokradiyya.

Karanta Wannan  Hotunan Kafin Auren Diyar Gwamnan Jihar Katsina, Hajia Aisha Dikko Radda Da Angonta, Ahmad Usman (Inuwar Ƙasar Hausa)

Hakan na zuwane yayin da ake rade-radin kasar Amurka na shirin shiga fadan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *