Wednesday, January 15
Shadow

Masarautar Kano: Yajin aiki ya hana sauraron ƙarar Aminu Ado

A jihar Kano da ke arewacin Najeriya, yajin aikin da ƙungiyar ƙwadago ta fara a yau ya kawo cikas wajen zaman sauraron ƙarar da Alhaji Aminu Babba Danagundi ya shigar yana ƙalubalantar rushe masarautun jihar.

Gwamna Abba Kabir ya soke masarautu biyar – ciki har da sababbi da aka ƙirƙiro a 2019 – bayan sauye-sauyen da Majalisar Dokokin Kano ta yi wa dokar masarautun jihar a watan Mayu, wanda hakan ya ba shi damar sauke Sarki Aminu Ado Bayero, kuma ya naɗa Muhammadu Sanusi II.

Sai dai bayan ɗaukar matakin ne Aminu Ado Bayero ya koma garin kuma ya sauka a gidan sarki na Nassarawa saboda umarnin kotu da ya ce a dakatar da rushe masarautun har sai ta gama sauraron ƙarar.

Karanta Wannan  Kai Talaka Da Kake Ta Tada Jijiyar Wuya Kan Ŕìķìçìn Masarautar Kano, Ina Kake A Cikin Wannan Hoton?

“Da zarar an janye yajin aiki kotu za ta ba mu sabuwar ranar sauraron ƙarar, umarnin da kotu ta bayar yana nan daram dam, yana nan yana aiki,” in ji lauyan masu shigar da ƙara Muhammad Said Waziri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *