
Masu garkuwa da mutane sun sace wata mata me shekaru 60 da haihuwa a Asibitin mahaukata dake Dawanau, Karamar hukumar Dawakin Tofa Kano.
Matar me suna Talatu Ali an yi garkuwa da itane a yayin da take jiran ganin Likita.
Dan matar da dan uwanta ne suka kai ta Asibitin, saidai a yayin da suma suke jiran layi ya zo kanta taga likita, sai suka nemeta sama da kasa suka rasa.
Lamarin ya farune ranar February 19, 2025 da misalin karfe 8 na safe, saidai ranar February 21 da misalin karfe 7 na safe an kira danginta inda aka tabbatar musu da cewa an yi garkuwa da itane.
Hukumar ‘yansandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin.