Saturday, December 13
Shadow

Masu gudanarwa na jami’o’in Najeriya sun sace Naira Biliyan 71.2 daga cikin kudaden da aka bayar a baiwa daliban jami’o’in bashi

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa ƙasar almundahana, ICPC ta ƙaddamar da wani bincike kan zargin zabtare wa ɗaliban da gwamnati ta bai wa bashin karatu da ake kira NELFUND da makarantu da jami’o’i ke yi.

Hukumar ta ICPC wadda ta wallafa hakan a shafinta na X, ta ce w annan dai ya biyo bayan rahotannin da ke zargin manyan makarantu fiye da 51 da ke datse kuɗaɗen.

An dai yi zargin cewa manyan makarantun na datse kuɗin da ya kai naira 3,500 zuwa naira 30,000 daga kuɗin bashin kowane ɗalibi.

Binciken farko-farko ya bayyana yadda aka samu giɓi a rabon kuɗaɗen, inda daga cikin naira biliyan 100 da gwamnatin tarayya ta saki ga tsarin bayar da bashin na NELFUND, naira biliyan 28.8 ne kacal suka isa ga ɗaliban, inda kuma aka nemi naira biliyan 71.2 aka rasa.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna: Uwargidan Gwamnan Bauchi, Hajiya Aishatu Bala Mohanmed (Sarauniyar Bauchi) Kenan A Cikin Kicin Tana Girki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *