Tuesday, September 22
Shadow

Gwamnonin arewa maso gabashin Najeriya na taro kan tsaro a yankin

A ranar Litinin ɗin nan ne gwamnonin shiyyar arewa maso gabashin Najeriya suke taro a birnin Damaturu babban birnin Jihar Yobe kan matsalolin da yankin ke fama da su.

Taron na zuwa a daidai lokacin da yankin ke fama da sabin hare-haren mayakan Boko Haram.

Masana da al’ummar yankin na cewa dama ce gwamnonin suka samu domin tattauna yadda za a shawo kan matsalar tsaro da ke addabar yankin.

A ranar Talata ne dai ƙungiyar ISWAP ta ɗauki alhakin kai wani harin bam da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 26 a Rann a jihar Borno.

Karanta Wannan  Lauya ya baiwa NBC wa'adin kwanaki 30 da ta soke ko kuma hana bàtssà a shirin BB9ja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *