
Rahotanni da hutudole ke samu na cewa Rundunar sojojin Najeriya ta fito da daya daga cikin rundunar sojojin ta mafi karfi da bayar da sakamakon da ake so wajan yaki inda aka kaisu Arewa maso gabas.
Sunan rundunar shine 134 Special Forces Battalion Wanda a baya sun yi yaki tare da rundunar sojoji da Najeriya ta dauoo haya daga kasar Afrika ta Kudu a shekarar 2013 suka yaki Boko haram,.
Rundunar ta kuma taba yaki a Kangarwa dake jihar ta Borno a lokacin da aka yi fama da ‘yan Bindiga wadanda ba B0k0 Hàràm ba kuma ta gama dasu.
Sannan a shekarar 2019, sun kuma yaki B0k0 Hàràm inda kuma suka yi nasara.
Hakanan a shekarar 2022 an kai rundunar jihar Kaduna inda ta yaki ‘yan Bindiga a camma kuma ta yi nasara.
Sojojin dake Arewa maso gabas rahotanni sun bayyana cewa sai murna suke da wannan lamari.