
A yayin da ake shirin yin sallar Layya, Masu sayar da Raguna da yawa na kokawa da rashin ciniki.
Farashin ragunan ya tashi sosai musamman saboda karancinsu da kuma matsalar tsaro da yankin Arewa ke fama dashi.
Wani me sayar da rago a kasuwar Dei-Dei dake Abuja me suna Ahmed Mai-Samari yace kulle iyakar Najeriya da Nijar da hana shigo da ragunan ya taimaka wajan hauhawar farashin ragunan.
Yace hakan yasa ragunan da aka kai kasuwanni sun yi kadan sosai wanda hakan yasa farashinsu ya tashi musamman idan aka kwatanta da shekarar 2024.
Yace yanzu yawanci ragunan sun nunka kudinsu, wanda a shekarar data gabata aka sayar akan Naira dubu 200 yanzu sai mutum yasa Naira Dubu 400.
Yace mafi karancin rago yanzu ana sayar dashi a farashin Naira 150,000 zuwa 190,000. Yace tsaka-tsaki ana sayar dashi a farashin Naira 200,000 zuwa 250,000, yace sauran kuma ana sayar dasu akan farashin Naira 350,000 har zuwa Naira Miliyan 1.
Shima wani me sayar da ragunan a kasuwar Dutse, Mr Sanusi Abdullahi ya bayyana cewa, farashin Rago a yanzu daga Naira 200,000 ne zuwa Naira 700,000.
Yace dole gidaje da kauyuka suke bi suke sayi ragunan a hannun mutane saboda rashin kawosu daga kasar Nijar.
Ya bayyana cewa raguna 120 ya kai kasuwar amma zuwa yanzu 7 kawai ya sayar amma yana fatan sayar da ko da rabine kamin sallah ko da ba’a akan riba me yawa ba.
Hakanan shima wani Malam Mustapha Aminu me sayar da ragunan a kasuwar Bwari yace bana ba kasuwa duk da yake cewa farashin rago mafi karanta Naira 100,000 ne.
Yace bara sun sayar da raguna da yawa duk da ana wahalar amma bata kai ta bana ba, yace amma bana abin yayi muni.
Wani me sayen ragon yace dan akuya ya saya maimakon rago tunda yanzu baya iya sayen Ragon.