
Rahotanni sun bayyana cewa, masu shirya zanga-zangar neman a saki shugaban Haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu a yau Litinin, Sun ce ba gudu ba ja da baya duk da gargadin da jami’an tsaro suka musu.
Masu zanga-zangar sun shirya yin tattaki zuwa fadar shugaban kasa dan neman a saki Nnamdi Kanu.
Hakan kuma na zuwane a yayin da Babbar kotun gwamnatin tarayya ta hana masu zanga-zangar zuwa kusa da fadar gwamnati ko kuma kuma majalisar tarayya ko duk wani ginin gwamnati.
Saidai duk da wannan, masu zanga-zangar sun ce ba gudu ba ja da baya, hakanan shugaban Zanga-zangar, Omoyele Sowore yace maganar umarnin Kotun ba gaskiya bane.
Idan dai masu zanga-zangar suka fito, akwai yiyuwar za’a yi dauki ba dadi tsakaninsu da jami’an tsaro.