Tuesday, November 18
Shadow

Masu shirin Yin Zqngq-Zqnzqr neman a Saki Nnqmd1 Kqnu sun ce ba gudu ba ja da baya duk da gargadin jami’an tsaro

Rahotanni sun bayyana cewa, masu shirya zanga-zangar neman a saki shugaban Haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu a yau Litinin, Sun ce ba gudu ba ja da baya duk da gargadin da jami’an tsaro suka musu.

Masu zanga-zangar sun shirya yin tattaki zuwa fadar shugaban kasa dan neman a saki Nnamdi Kanu.

Hakan kuma na zuwane a yayin da Babbar kotun gwamnatin tarayya ta hana masu zanga-zangar zuwa kusa da fadar gwamnati ko kuma kuma majalisar tarayya ko duk wani ginin gwamnati.

Saidai duk da wannan, masu zanga-zangar sun ce ba gudu ba ja da baya, hakanan shugaban Zanga-zangar, Omoyele Sowore yace maganar umarnin Kotun ba gaskiya bane.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Ba zamu fasa yin Tinubu ba, kuma mu Hausawa da ke yin Tinubu mun fi masa Yarbawan da basa yinsa>>Inji Sheikh Sani Yahya Jingir

Idan dai masu zanga-zangar suka fito, akwai yiyuwar za’a yi dauki ba dadi tsakaninsu da jami’an tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *