Thursday, January 16
Shadow

Masu zanga-zanga sun je majalisar tarayya suna neman a kori shugaban NNPC Mele Kolo Kyari daga aiki

Wasu kungiyoyin dake ikirarin fafutuka sun je majalisar tarayya suna neman a kori shugaban Kamfanin mai na kasa, NNPCL Mele Kolo Kyari daga aiki.

Sun kuma nemi a yi bincike dan gano masu yiwa shirin gyaran matatun man fetur zagon kasa a Najeriya.

Sun ce shugabancin Mele Kolo Kyari ya yiwa Matatun man fetur na Najeriya illa sosai.

Shugaban kungiyar, Segun Adebayo, ya jawo hankalin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya jawa shugabancin kamfanin man fetur din na kasa, NNPCL kunne kan kasa su kara daukar wasu matakai da zasu kara jefa tattalin arzikin kasarnan cikin matsi.

Kungiyar tace Najeriya zata iya tace man da za’a yi amfani dashi a cikin kasarnan amma saboda zagon kasa an hana hakan faruwa.

Karanta Wannan  Gwamnatin tarayya ta baiwa masu boye da dalar Amurka a gidajensu watanni 9 su fito da ita

Ta kara da cewa Misali ga Aliko Dangote ya bude matatar man fetur amma masu zagon kasa a NNPCL suna kokarin hanashi aiki yanda ya kamata.

Kungiyar tace sun san shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu yana son Najeriya dan hakane ma suke kiransa da ya sanya baki dan kada a durkusar da tattalin arzikin kasarnan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *