Saturday, January 4
Shadow

Matafiya na shan wuyar sayen tikitin jirgin kasan Abuja-Kaduna ta intanet

Duk da shigo da tsarin sayan tikitin shiga jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna ta intanet da gwamnatin Najeriya ta yi a shekarar 2021, har yanzu fasinjoji na shan dan karen wuya kafin samun shi.

Tsohon ministan sufurin kasar Rotimi Amaechi ne ya fito da tsarin a zamanin mulkin tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari, da nufin magance cuwa-cuwar saida tikitin da ake zargin ma’aikatan wurin na yi.

Gwamnatin Najeriya ta kashe naira miliyan 900 domin inganta hakan, sai dai bincike na baya-bayan nan da jaridar Solacebase ta fitar, ta raiwato a tashar jirgi ta Idu da Kubuwa a Abuja babban birnin kasar ya nuna bata sauya zani ba.

Karanta Wannan  WATA SABUWA: Harajin da ƴan Nijeriya ke biya ya yi kadan – Bill Gates

Dubban matafiyan da a kowacce rana suka dogara da jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna na shan dan karen wuya kafin samun tikitin, ko dai dalilin rashinsa a intanet, ko rashin kyawun sadarwa, da kuma zargin ma’aikatan wurin da yin makarkashiyar.

Matsalar tsaro da ake fama da ita a arewacin Najeriya, da satar mutane domin neman kudin fansa musamman tsakanin Abuja zuwa Kaduna na daga cikin dalilan da yawancin matafiya suka dogara da jirgin kasa ko na sama ga mai hali domin isa inda suka nufa cikin aminci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *