Tuesday, January 20
Shadow

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya je jihar Benue inda zai halarci daurin auren dan sakataren Gwamnatin tarayya, George Akume

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya je jihar Benue inda yake wakiltar shugaban kasar wajan daurin auren dan sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume.

Za’a daura aurenne tsakanin Samuel Aondoakura da Deborah Ershim.

Sakataren Gwamnatin tarayyar, George Akume da Gwamnan jihar Benue, Dr. Hyacinth Alia da sauransu ne suka tarbi shugaban kasar.

Sanarwar ta fito ne daga bakin me magana da yawun mataimakin shugaban kasar, Stanley Nkwocha.

Hakan na zuwane kasa da sati daya bayan da shima sakataren Gwamnatin Tarayyar, George Akume ya auri matarnan me yawan auren manyan mutane watau Zainab wadda ta tabata auren gwamna, Sanata, Basaraken Yarbawa da Wani Balarabe dan gidan sarauta.

Karanta Wannan  Atiku ya nemi Peter Obi ya zama mataimakinsa a 2027 dan su kwace mulki a hannun Tinubu, inda shi kuma yayi Alkawarin yin mulki sau daya ya sauka ya barwa Peter Obin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *