
Mata magoya bayan Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu sun bayyana takaici da jin Haushin watsi da aka yi dasu bayan da sukawa shugaban kasar yakin neman zabe.
Matan sun nemi a sakasu cikin bayar da mukamin da shugaban kasar yake yi.
Matan wadanda suka fito daga jihar Bayelsa sun bayyana hakane ta bakin wakiliyarsu a Abuja ranar Litinin.
Tace a cikinsu akwai kwararrun mata da zasu taimaka wajan cimma muradun gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu idan aka basu dama.
Ta bayyana takaicin yanda aka rasa mata a mukaman siyasa a Gwamnatin Tinubu duk da rawar da suka taka wajan yakin neman zabensa.