
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi Tuntube inda ya kusa faduwa yayin da yake hawa matakalar jigin saman sa na Airforce One.
Irin wannan lamari ya taba faruwa da tsohon shugaban kasar, Joe Biden inda akai ta masa tsiya da cewa tsufa ne ya masa yawa.
Yanzu dai ‘yan jam’iyyar Republicans dole bakinsu zai kulle saboda sune dama ke sukar Biden saboda hakan.