
Matar gwamnan jihar Borno, Dr. Falmata Babagana Zulum ta karrama Faiza Abdullahi wadda karamar ma’aikaciyace dake daukar Albashin Naira dubu 30 bayan da ta mayar da Naira Miliyan 4.8 ds aka tura mata bisa kuskure.
Hakanan matar gwamnan ta bata kayan abinci da sauran kyautuka.
Faiza dake aiki a jami’ar Maiduguri, UNIMAID ta bayyana cewa ta mayar da kudin da aka tura mata ne saboda tsoron Allah.