
Hukumar sojojin Najeriya ta sanar da daukar matasa guda 24,000 a cikin watanni 6 masu zuwa dan magance matsalar tsaron data addabi Najeriya.
Hakan ya fito daga bakin shugaban sojojin kasa, Lieutenant General Waidi Shaibu ne a yayin ziyarar da ya kai rundunar sojoji ta 1 dake kaduna ranar Laraba.
Ya bayyana cewa, zasu yi amfani da guraren horas da sojoji guda 3 da ake dasu wajan horaa da sojojin.
Ya bayyana bukatar karin sojoji dan magance matsalar tsaro da ake fama da ita.
Hussaini dahiru baure
[email protected]