
Wata matashiya a garin Gubio na jihar Borno ta Khashye kanta saboda mahaifinta ya tursasa mata sai ta auri abokinsa.
Rahotan yace lamarin ya farune ranar lahadi da misalin karfe 6:20 na yamma.
Matashiyar dai tana da wanda take so amma mahaifinta ya tursasa mata sai ta auri wanda bata so.
Wani ma’aikacin sa kai a garin ya bayyana cewa lamarin ya jefa mutane cikin jimami.