
Matashiya me suna Opesusi Faith Timilehin ‘yar Kimanin shekaru 19 ta sha guba ta kashe kanta ranar Litinin saboda ta ci maki 190 a jarabawar JAMB.
Faith na zaunene da yayarta a Legas amma ‘yar asalin Abeokuta ce, makwabtansu sun bayyana ta a matsayin mutuniyar kirki wadda bata son hayaniya.
Danginta sun ce ko a shekarar data gabata ta rubuta jarabawar JAMB amma makinta na shekarar data gabata ya fi na yanzu.
Saidai wani abin tashin hankali shine an bata Admission bayan mutuwarta.