Wednesday, April 29
Shadow

Matashiya ta Kàshè kanta saboda bata ci maki me yawa a jarabawar JAMB ba

Matashiya me suna Opesusi Faith Timilehin ‘yar Kimanin shekaru 19 ta sha guba ta kashe kanta ranar Litinin saboda ta ci maki 190 a jarabawar JAMB.

Faith na zaunene da yayarta a Legas amma ‘yar asalin Abeokuta ce, makwabtansu sun bayyana ta a matsayin mutuniyar kirki wadda bata son hayaniya.

Danginta sun ce ko a shekarar data gabata ta rubuta jarabawar JAMB amma makinta na shekarar data gabata ya fi na yanzu.

Saidai wani abin tashin hankali shine an bata Admission bayan mutuwarta.

Karanta Wannan  Sakataren ma'aikatar gwamnati da aka dakatar a jihar Kebbi Dr. Nasiru Abubakar Kigo ya janye ikirarin da ya yi na yawan masu auren jinsi a jihar Kebbi da Sokoto, kalaman da ya janyo masa dakatarwar daga gwamnan jihar Nasir Idris

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *