
Mijin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, Emmanuel Oritsejolomi Uduaghan ya magantu game da rikicin da ke tsakanin matarsa da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
Mijin, wanda basarake ne a yankin Neja Delta ya ce matarsa ta faɗa masa lokacin da Akpabio ya ci zarafinta, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
“Da kaina na je na same shi na buƙaci ya ba matata girman da ta cancanta, sannan ya girmama abotan da ke tsakaninmu. Bayan mun tattauna sai muka amince da a warware maganar cikin mutunci.
“Amma bayan maganar da muka yi, sai matata ta cigaba da bayyana damuwa game da irin cin zarafin da take fuskanta daga shugaban majalisar dattawar.
“Ni dai na yarda da matata, kuma aure muka yi na soyayya da ƙauna. Babu abin da ya fiye min ita a yanzu domin ita ce farin cikina.”