
Matatar Man fetur din Dangote ta kara farashin man fetur dinta a gidan man MRS dake Abuja zuwa Naira 950 akan kowace lita.
Rahotanni sun ce ranar Talatar data gabata, Gidan man na MRS dake Abuja na sayar da man sa akan Naira 851 kan kowace lita amma zuwa ranar Laraba sai aka ga sun canja farashi zuwa 950.
Hakanan sauran gidajen man dake da alaka da Dangote irin su Ardova da Optima suma sun canja Farashin nasu zuwa sama.
Daya daga cikin manajojin gidan man MRS ya shaidawa kafar Daily Post cewa, matatar man Dangote ta kara farashin da take sayarwa da ‘yan kasuwa man.