
Rahotanni sun bayyana cewa, matatun man fetur na kasashen Turai sun fara kullewa saboda kafuwar matatar man Dangote da kuma yanda kasashen Afrika suka koma sayen man fetur a hannun matatar man ta Dangote maimakon sayowa a kasashen turai.
Rahoton ya bayyana cewa a baya kamin zuwan matatar Dangote, matatun man kasashen Turai na samar da man fetur ganga miliyan 4.207 amma yanzu saboda zuwan matatar man fetur din Dangote, ganga Miliyan 4.104 suke fitarwa.
Hakan ya farune sanadiyyar rufewar matatun man fetur irin su, Grangemouth refiner dake Scotland, da Prax’s da sauransu.