Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi zargin cewa magabacinsa, Bello Matawalle, na da hannu dumu-dumu a aiyukan ƴan fashin jeji da suka addabi jihar.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa da ya ke magana a wani shirin siyasa na gidan talabijin na TVC a daren jiya Laraba, gwamnan ya yi ikirarin cewa, bisa bayanan da su ka samu, magabacinsa ya jagoranci gwamnatin da ke hada kai da ƴan fashin jeji su na aikata ta’addanci.
Lawal ya kuma zargi gwamnatin da ta shude a karkashin Bello Matawalle, wanda a yanzu shi ne karamin ministan tsaro da karkatar da kudaden jihar da kuma yin sakaci da harkar tsaro a jihar.
“Eh, akwai batutuwa da yawa a baya daga gwamnatin da ta gabata. A gaskiya, bari in fadi wannan sarai: da nine shi (Matawalle) zan yi murabus in fuskanci duk wani zargi da ake min, hakan shi ne mutunci a tare da shi..
“Daga dukkan bayanan da muke samu, magabaci na (Matawalle) na da hannu dumu-dumu a wasu daga cikin wadannan al’amuran na ‘yan fashin jeji” in ji Lawal.
Da ya ke tabbatar da ikirarin da ya yi na cewa magabacinsa na da hannu a ‘yan fashin jeji, ya bayyana yadda wani sakatare na dindindin a gwamnatin Matawalle ya biya kudin fansa ta gidan gwamnati domin a sako ‘ya’yansa da ‘yan bindiga su ka sace,” in ji shi.