Wani matukin jirgin saman Turkish Airlines ya mutu a yayin da yake tuka jirgin a sararin samaniya.
Hakan yasa dole sauran matukan jirgin dake tare dashi suka karkatar da akalar jirgin zuwa birnin New York na kasar Amurka.
Lamarin ya farune da safiyar ranar Laraba a yayin da jirgin ya tashi daga Seattle zuwa Istanbul.
Matukin jirgin me suna Capt. İlçehin Pehlivan ya samu matsalar kidimewar gigin mutuwa yana tsaka da tuka jirgin.
Saidai akwai sauran matuka jirgin 2 dake tare dashi inda suka yi gaggawar sauke jirgin a filin jirgi na John F. Kennedy International Airport dake birnin New York.
Kamfanin jirgin ya tabbatar da cewa, Capt. İlçehin Pehlivan ya mutu ne kamin jirgin ya sauka kasa.
Kamfanin ya kara da cewa lokaci na karshe da aka duba lafiyar Capt. İlçehin Pehlivan shine a watan Maris na 2024 kuma ba’a ga wata rashin lafiya da zata iya hanashi ci gaba da aikinshi ba.
Kamfanin ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin me shekaru 59 wanda ya fara aiki da kamfanin na Turkish Airlines a shekarar 2009.
Hakanan kamfanin yace nan gaba kadan zasu samar da jirgin da zai kwashi fasinjojin zuwa Istanbul daga birnin New York inda aka ajiyesu.