
Tauraruwar fina-finan Kudu, Bimbo Akintola ta bayyana cewa, maza sun yi karanci dan haka dolene mata su hakura a rika yin auren mata 4.
Tace hakan ne zai kawo saukin dadewar mata da suke yi a gidajen iyayensu ba tare da aure ba.
Ta bayyana cewa, bayan haka ma auren mace fiye da daya al’adar Yarbawa ce dan haka ya kamata a ci gaba da dabbaka wannan al’ada.