Thursday, July 16
Shadow

DJ ya dakatar da kida bayan da aka hanashi Abinci a wajan taro

Wani DJ me saka kida, ya dakatar da kida a wajan bikin da ya je bayan da aka hanashi abinci yayin da ake ta baiwa sauran mutanen abinci.

DJ din ya dakatar da kidan sannan ya kashe Janareta dan ya nuna fushinsa.

A wani Bidiyonsa da ya watsu a kafafen sada zumunta, an ga DJ din yana kumfar baki da fadin cewa, ba’a masa adalci ba.

Saidai daga baya an bashi baki inda aka masa alkawarin samar masa da abinci da zai ci.

Karanta Wannan  Dan Majalisa Mai Wakiltar Fagge Kenna A Zauren Majalisar Wakilai, Barista MB Shehu A Saman Bishiya Yana Sa Ido Kan Zaben CIke Gurbi Dake Gudana A Shanono

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *