Masara na da matukar amfani sosai a jikin mutum inda ake amfani da ita wajan yin abubuwan amfani da yawa na yau da kullun.
Tana Gyara ido: Masara na da sinadarai irin su carotenoids, da lutein, da zeaxanthin wanda sune ke taimakawa wajan gyaran ido da kara karfinsa.
Masara na taimakawa abinci narkewa a cikin jikin mutum musamman saboda fiber dake cikinta.
Hakanan tana taimakawa maza sosai wajan karin lafiyar maraina.
Masara na taimakawa masu fama da matsalar mantuwa.