Sunan Awara da turanshi shine Soybean cake.
Awara na daya daga cikin abunci masu arha da ake amfani dasu wajan kawar da yunwa cikin gaggawa a arewacin Najeriya.
Hakanan ana cin awara dan marmari.
Kasancewar ana amfani da waken suya ne wajan yinta, yana taimakawa sosai wajan gina jiki.