Monday, May 5
Shadow

Motar kaya ta hàlalàkà masu bikin Easter biyar a jihar Gombe

Wani hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutum biyar yayin da wasu takwas suka ji raunuka a ƙaramar hukumar Billiri ta jihar Gombe.

Lamarin ya faru ne a lokacin da birkin wata mota ɗauke da kayan abinci ya shanye, inda ta kutsa cikin dandazon jama’a da ke gudanar da bukukuwan Easter na mabiya addinin Kirista.

Wata da ke halartar bukukuwan kuma ta shaida lamarin ta faɗa wa BBC cewa ɓacin rai ya sa mutane suka ƙona motar nan take.

“Ana rawa ana waƙa ana biki, kawai sai mutane muka gani a ƙarƙashin mota, ana cewa ya tsaya ya tsaya amma bai tsaya ba,” in ji ta.

Karanta Wannan  Najeriya ta fada Duhu yayin da matsalar wutar lantarki ta sake aukuwa, Ji Jihohinnda lamarin ya shafa

“An ƙona komai da komai na motar, har sai da jami’an tsaro suka zo suka kori mutane.”

Rundunar ‘yansanda a jihar ta ce cikin waɗanda suka jikkata har da wasu Musulmai da ke sallah a gefen titi.

Ismaila Uba Misilli, shi ne babban jami’in yaɗa labarai na gwannan jihar ta Gombe. Ya ce zuwa yanzu hankula sun kwanta a yankin kuma an ci gaba da harkoki kamar yadda aka saba.

Gwamnatin jihar Gombe ta ɗauki nauyin kudin magunguna na ɗaukacin waɗanda suka ji raunuka sakamakon ibtila’in.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *