Tuesday, May 19
Shadow

An dakatar da wasannin gasar Serie A ta Italiya sanadiyyar rasuwar fafaroma

An dakatar da wasanni guda huɗu na gasar Serie A ta ƙasari Italiya bisa rasuwar Fafaroma Francis.

A ranar Litinin fadar Vatican ta sanar da rasuwar fafaroman wanda ya shafe shekara 88 a duniya bayan wata jinya da ya yi har aka kwantar da shi a asibiti.

Karawar da aka soke ta haɗa da:Torino v Udinese, Cagliari v Fiorentina, Genoa v Lazio and Parma v Juventus.

Hukumar da ke lura da gasar ta Serie A a ƙasar ta ce za ta duba wani lokacin da za a buga wasannin a nan gaba.

Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da dama sun miƙa ta’aziyyar su bisa rasuwar shugaban cocin katolikan na duniya.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon Abinda matasa a jihar Edo sukawa fastar yakin neman zaben shugaba Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *