Wednesday, January 15
Shadow

Mu Rungumi Tsarin Amfani Da CNG A Motocinmu Maimakon Man Fetur Za Mu Sauki

Daga Aliyu Samba

Da ace mutane zasu rungumi tsarin amfani da Compressed Natural Gas (CNG) a motocin su maimakon Fetur, da an samu sauki fiye da yadda ake zato. An kawo wannan cigaban har da samar da conversion centers a dukkan shiyyoyin kasar nan, mu yan Northwest, namu yana Kakau dake jihar Kaduna.

CNG ya fi sauƙi akan fetur da kaso 40 cikin 100, kuma gas ne da baya kamawa da wuta kamar LPG na girki, ba kuma ya hayaki da ke cutarwa, haka kuma akwai arzikin sa a ƙasar nan fiye da yadda ake zato. Akwai buƙatar mutane su rungumi tsarin dan hutawa daga hauhawar farashi da ake samu kan fetur sakamakon yadda kamfanin samar da mai na ƙasa ke fuskantar kalubale kala kala.

Karanta Wannan  A karin farko, Shugaba Tinubu ya sakawa dokar haramtawa sojojin Najariya yin Luwadi, Madigo da shan giya

Wannan tsarin na CNG yafi sauki, kuma bashi da wata matsala ga ababen hawa. A kwanaki ma naga gwamnati ta cire duty ga duk motar CNG da za a shigo da ita daga ƙasar waje. Muna da wuyar karɓar sabon cigaba, amma wannan cigaban zai sama mana sauƙi a ɓangaren sufuri da kuma inganta walwalar masu ababen hawa takan kashe kuɗi kaɗan da samun biyan buƙata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *