Tsohon me magana da yawun shugaban kasa, Doyin Okupe ya bayyana cewa su yarbawa ba zasu kara yadda a rika zagin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba.
Yace Tinubu dan lelene a wajansu.
Ya bayyana hakane a hirar da gidan talabijin na Channels TV suka yi dashi.
Saidai yace idan abubuwa a yanzu basa tafiya yanda ya kamata a yi hakuri nan gaba komai zai daidaita.