
Tsohon me magana da yawun Peter Obi, Kenneth Okonkwo, ya bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne zai sake cin zabe muddin ‘yan ADC suka tsayar da dan kudu takara a zaben 2027.
Yace dan Arewa a tsakanin Atiku Abubakar ko Aminu Waziri Tambuwal ko Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne ya kamata a tsayar takara.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV inda yace dan Arewa zai goyi baya a zaben na 2027.
Ya kara da cewa, kamata yayi a zabi wanda ke da karbuwa a Arewa sosai.