
Itama dai Kungiyar Ohanaeze Indigbo reshen matasa,OYC ta bayyana cewa, bata son kawo harin da kasar Amurka zata yi zuwa Najeriya.
Kungiyar tace maimakon haka, tana neman kasar Amurka ta taimaka musu a gudanar da zaben jin ra’ayi dan a raba Najeriya a basu kasarsu.
Kungiyar ta bakin shugabanta, Comrade Igboayaka O. Igboayaka tace ba ita kadai bace hadda kungiyar Jihohin dake tsakiyar Najeriya duk suna neman a yi zaben ba raba gardama dan a raba kasarnan.