
Hukumar Bayar da Bashin Karatu ta Najeriya Nelfund ta ce ta ba ɗaliban Najeriya rancen kuɗi naira biliyan 56.55 domin biyan kuɗin makaranta da alawus ɗin kashewa na yau da kullum.
Hukumar ta bayyana haka ne domin bayyana nasarorin da ta samu a cikin shekara ɗaya da fara aiki tun bayan ƙirƙirar shirin.
A wata sanarwa da daraktan sadarwa na hukumar, Oseyemi Oluwatuyi ta fitar, ya ce sama da ɗalibai 600,000 ne suke nami rancen, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
“Bayan tantancewa, mun amince tare da ba ɗalibai 550,000 rancen, inda muka ba su kuɗi naira biliyan 56.85 a cikin shekara guda.”
“Tsarin bayar da rancen ya taimaka wajen sauƙaƙa wa ɗaliban Najeriya da iyaye,” in ji ta.