Friday, August 7
Shadow

Mun gano Dalibai na karyar cewa su Zabaya ne dan su yi satar Amsa>>Hukumar Jarabawar JAMB

Hukumar shirya jarabawar share fagen shiga Jami’a JAMB ta bayyana cewa, ta gano wata dabarar satar Amsa wadda dalibai ke karyar cewa su zabayane dan yin satar Amsar.

Shugaban hukumar, Professor Ishaq Oloyede ne ya bayyana hakan inda yace yawan daliban da suka yi rijistar Jarabawar a matsayin Zabaya sun yi yawa, shiyasa suka ce bari su yi bincike.

Yace da suka yi bincike sai suka gano ashe wata fasahar zamani ce aka zo da ita ta satar amsa wadda kuma idan daliban basu yi karyar cewa, su Zabaya bane ba za’a barsu su rubuta jarabawar ba.

Yace daga baya sun gano irin wadannan dalibai kuma ya jawo hankalin sauran daliban su kaucewa irin wannan lamari.

Karanta Wannan  Wallahi Sharri aka kala min ban zaghi Shugaban Amurka, Donald Trump ba, Inji Sanata Godswill Akpabio bayan da wani Rahoto ya bayyana dake cewa ya gayawa Trump maganganu marasa dadi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *