
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ta kasa, EFCC tace a yanzu masu satar dukiyar Gwamnati da Crypto Wallet suke amfani suna boye kudaden da suka sata.
Shugaban hukumar, Ola Olukoyede ne ya bayyana hakan.
Yace sun gano yanda lamarin ke ta kara yaduwa tsakanin barayin gwanatin.
Ya bayyana hakane a wajan wani taro da ya wakana a Abuja da Legas ranar Alhamis.
Yace zuwan Crypto ya kawo ci gaba amma kuma ya kawo wa barayi hanyar boye kudaden da suka sata.