
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, jami’an tsaro sun samar da tsaro sosai a yankin Arewa maso gabas da Arewa maso yamma.
Yace Mutanen da a baya suka tsere daga gidajensu saboda matsalolin tsaro a yanzu sun koma gidajen nasu.
Shugaban yace an samu nasarori sosai a yaki da masu dauke da makamai a sassa daban-daban na kasarnan.
Shugaban ya bayyana hakane yayin da yake jawabin ranar cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yanci.