
Jam’iyyar ADC ta gamayyar ‘yan Adawa ta bayyana cewa, ba lallai ta yi yakin neman zabe ba dan kuwa halin matsi da yunwar da ‘yan Najeriya ke ciki ta isa tasa su zabeta.
Sakataren jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi dashi.
Yace kusan an musu rabin yakin neman zaben da ya kamata su yi saboda yunwar da ake fama da ita inda yace abinda ya rage musu shine su nunawa ‘yan Najeriya cewa zasu iya fitar dasu daga halin kuncin da aka sakasu ciki.
Yace a bayyane yake cewa, ‘yan Najeriya basa son Jam’iyyar APC saboda wahalar data basu.