Kananan yaran da aka kama aka gurfabar a kotu bisa zargin cin amanar kasa da yunkurin kifar da gwamnatin shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu amma Shugaban ya yafe musu sun koma gida Kano.
Kamin komawarsu, sai da suka je fadar shugaban kasa suka gana da mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima inda ya bayyana musu cewa suna da Bidiyo da hotuna dake nuna cewa sun aikata laifi amma tausayi irin na shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne yasa ya yafe musu.
Ya bayyana cewa zanga-zangar tsadat rayuwa ta jawo asarar Naira Biliyan 300.
Ya jawo hankalin matasan da cewa kada su yadda ayi amfani dasu wajan tayar da fitina inda yace wannan dama ce da suka sake samu ta su zama na gari.
Tuni dai aka mika su hannun gwamnan jihar ta Kano Abba Kabir Yusuf ina shima ya daukesu zuwa gida.