Friday, December 6
Shadow

Najeriya ta fada Duhu yayin da matsalar wutar lantarki ta sake aukuwa, Ji Jihohinnda lamarin ya shafa

‘Yan Najeriya sun fada duhu biyo bayan sake samun matsala da wutar lantarkin kasar ta yi.

Wannan shine karo na 3 da wutar lantarkin kasar ke samun matsala a shekarar 2024.

Da Misalin karfe 1:50 pm. Na ranar Talata ne wutar lantarkin ta sake samun matsala.

Kamfanin kula da wutar na kasa,TCN ya tabbatar da hakan amma yace ba gaba daya wutar bace ta samu matsala.

Kakakin hukumar, Ndidi Mbah ne ya tabbatar da hakan inda yace injiniyoyinsu na aiki tukuru dan dawo da wutar.

Ya kara da cewa An samu dawo da wutar a babban birnin tarayya Abuja kuma suna kokarin dawo da ita a sauran jihohi.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu Ya Tallafawa Ma'aikata Da Ɗalibai Da Gudummawar Motocin Sufuri

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *