Biyo bayan fara dawo da ci gaba da aikin matatar man fetur ta Warri, ‘yan kasuwar man fetur sun bayyana kyakykyawan zatom cewa, farashin man fetur din zai sauka.
‘Yan kasuwar sun ce yanzu gasa tsakanin masu matatun man fetur na cikin gida zata yi tsanani ta yanda dole za’a sauke farashin man fetur din.
Sun bayyana hakane ranar Litinin bayan fara aikin matatar man fetur ta Warri.
Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya bayyana cewa, zai fara fitar da man fetur din zuwa kasashen waje dan samun kudin shiga.
Hakan na zuwane wata daya bayan da matatar man fetur da Fatakwal ta fara aiki.