Sunday, March 23
Shadow

Matatar Man Dangote ta Tafka Asarar Naira Biliyan 32

Matatar Man Dangote zata tafka asarar Naira Biliyan 32 saboda sayar da Lita Miliyan 500 na man fetur a farashin man da ya karye.

Dangote da kansa ne ya sanar da karya farashin man fetur din inda kuma ya tabbatar da cewa suna da man fetur din ganga Miliyan 500 a cikin tankunansu.

Ya bayyana hakane a yayin da farashin man fetur din yake akan naita 890 kan kowace lita.

Idan aka sayar da man fetur din a tsohon farashin man na Naira 890 akan kowace lita, Dangote zai samu Naira Biliyan 445.

Saidai daga baya a watan Fabrairu Dangote ya sanar da rage Naira 65 daga farashin man wanda a yanzu ake sayarwa akan Naira 825 akan kowace lita.

Karanta Wannan  Ji yanda Wani dan jarida yawa Sanata Godswill Akpabio Tonin Sillili inda ya bayyana dalilin da ya zama dole a kama shi a daure a gidan yari

Idan aka sayar da Lita Miliyan 500 da Dangote yace suna da ita a ajiye akan sabon farashin na Naira 825 akan kowace lita, Dangote zai samu kudi Naira N412.5bn wanda hakan ke nufin ya tafka asarar naira Biliyan 32 kenan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *