Friday, December 5
Shadow

Munafurci Dodo: Rikici ya barke tsakanin Wike da Gwamna Makinde na jihar Oyo wanda sune suka hadewa Atiku kai suka ce ba zasu goyi bayanshi ba a zaben 2023

Rahotanni sun bayyana cewa rashin jituwa da rikici ya barke tsakanin Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde da Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Rahoton yace An kafa kwamiti dan yin sulhu tsakanin su amma Wike ya fice daga sulhun da ake yi inda ya ke zargin Gwamna Seyi Makinde da Gwamnan Jihar Enugu da hannu a rikicin da ya mamaye jam’iyyar.

Hakan na zuwane a yayin da jam’iyyar ke shirin yin babban taronta na masu ruwa da tsaki ranar 27 ga watan Mayu da muke ciki.

Tuni Kwamitin Amintattu na jam’iyyar suka kira taron gaggawa a yau, Litinin dan shawo kan matsalar.

Karanta Wannan  Ɓangaren Kwankwaso ba shi da hurumin korar mu daga NNPP saboda su ba halastattun shuwagabannin Jam'iyya bane- Kawu Sumaila

A zaben shekarar 2023 dai Gwamna Seyi Makinde da Nyesom Wike na daga cikin gwamnoni 5 da suka hadewa Atiku ka sukace ba zasu goyi bayansa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *