Friday, December 5
Shadow

Mutane 9 sun rasu sanadiyyar hadarin mota a jihar Jigawa

A kalla Mutane 9 ne suka rasu a hadarin mota da ya faru a kauyen Kyaramma dake karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa.

Hukumar ‘yansandan jihar ta tabbatar da faruwar hadarin inda tace ya farune da misalin karfe 2 na yamma tsakanin wasu motocin Golf 3 guda biyu wanda kuma ya bar mutane da yawa sun jikkata.

Kakakin ‘yansandan jihar, Shiisu Adam ne ya bayyana hakan inda yace motocin sun yi taho mu gama, yace bayan hadarin ‘yansandan sun kai dauki wajan inda suka kai wadanda suka jikkata Asibiti.

Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP A.T. Abdullahi, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan inda yace direbobi su rika kiyaye dokokin hanya dan gujewa hadarin.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: An ga Bilal Villa a daji dauke da Bìndyghà, lamarin ya jawo cece-kuce inda ya bayyana cewa sabuwar waka ce

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *