Wednesday, April 1
Shadow

Mutanen da kuka gani a wajan komawar Kwankwaso ADC kudi aka basu ba soyayyar gaskiyace ba>>Inji Gwamnatin Abba

Gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta bayyana cewa dubban mutanen da suka taru a wajan komawar Rabiu Musa Kwankwaso Jam’iyyar ADC kudi aka basu.

Kwamishinan yada labarai na Kano, Ibrahim Waiya ne ya bayyana haka a ganawarsa da AIT.

Yace sun san yanda ake yi, idan za’a yi taro ana bi kauyuka akwai wadanda ake baiwa kudi su rika tara maka mutane.

Yace a yanzu Abba ya shiga siyasar kasa inda yake damawa da sauran takwarorinsa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Duk wani dan Dariqa Shehu Tijjani ya bashi Aljannah, Abinda ya rage mai shine yayi aikin da shima zai ceci wasu>>Inji Wannan malamin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *