Wasu daga cikin mutanen dake zaune akan iyakokin Najeriya da Nijar sun shiga zullumi biyo bayan cece kucen da ya barke tsakanin kasashen biyu.
Shugaban mulkin soji na Jamhuriyar Nijar, Brig Gen Abdourahmane Tchiani ya zargi cewa Najeriya ta girke sojojin kasar Faransa tare da kafa sansanin yiwa ‘yan ta’adda atisaye.
Saidai me baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya karyata wannan zargi inda yace Babu inda Najeriya ta kafa sansanin sojojin kasashen waje.
Ribadu yace wannan kokari ne na kawar da hankalin mutane daga gazawar gwamnatin ta Jamhuriyar Nijar.
Da yake bayyana rashin jin dadinsa kan lamarin, wani mazaunin jihar Sokoto, Muhammad Illiyasu ya rantse da Allah cewa, cikin shekaru 30 da yake rike da sarautar Magajin garin Balle a karamar hukumar Gudu bai taba ganin sojojin Faransa ba.
Yayi kiran cewa kasashen Najeriya da Nijar su daidaita kansu dan su basa son tashin hankali da kasar Jamhuriyar Nijar.
Shima wani me sana’ar sayar da Shanu, Muhammad Altine dake zaune a garin Ruwa-Wuri dake karamar hukumar Tangaza ya bayyana cewa shekarunsa 20 yana wannan sanaa a wannan gari ama bai taba ganin Sojojin kasar Faransa ba.