
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, ya baiwa jami’an tsaron Najeriya umarnin su gaggauta kawo karshen matsalar tsaron da ake fama da ita ba tare da jinkiri ba.
Shugaban wanda yanzu haka yana kasar Faransa, ya bayyana hakane a sanarwar taya kiristoci murnar bukin Easter.
Shugaban yace karuwar matsalar tsaro da kashe-kashe na kwanannan ya matukar dameshi inda yace yana bayar da tabbacin samar da tsaro.
Sannan kuma ya mika sakon jaje ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa dasu inda yace yasan irin radadin da suke ji.
Shugaba yace ya kuma baiwa jami’an tsaro umarnin su gaggauta kawo karshen matsalar tsaro a kasarnan.