
Fasto Ebo Noah wanda ya ce wai an masa wahayi za’a yi tashin Qiyama ranar Kirsimeti, 25 ga watan Disamba amma ba’ayi ba, ya gargadi hukumomin kasar Ghana da suka kamashi.
Faston dai an kamashine saboda wannan abu da yayi ya dauki hankulan Duniya.
Saidai ya gargadi hukumomin kasar Ghana da cewa ya basu kwanaki 3 ko dai su sakeshi ko ya bace daga gidan yarin da ake tsare dashi.