Matashi Segun Olowookere wanda aka yankewa hukuncin kisa saboda satar kaza da kwan kazar a jihar Osun amma daga baya gwamnan jihar, Ademola Adeleke ya yafe masa ya bayyana yanda rayuwar gidan yari ta kasance masa.
Ya bayyana hakane a yayin ganawarsa da wakilin jaridar Punchng.
Segun ya kwashe shekaru 14 a gidan yari kuma tun yana dan shekara 17 aka kaishi gidan yarin.
Daya daga cikin labarin da ya bayar da yace yana damunshi shine yanda manya a gidan yarin ke lalata da kananan yara maza ta hanyar luwadi.
Yace daki daya da ya kamata ace mutane 10 ne zasu kwanta a ciki amma sai a tura mutane 50 a ciki.
Saidai yace a tsawon shekarun da yayi a gidan yari, bai bari yayi zaman banza ba, yayi karatu sannan yayi aiki tare da asibitin dake gidan yarin.